DAN UWA KADAINA SAKA 'PASSWORD'MAI SAUKI A'KOMAI NAKA

 

Dan Uwa yau nazo da wata shawara gareka, Ina baka shawara Aduk inda aka bukaci kasaka Password tofa karka yadda kasaka mai sauki misali pin din ka na banki, To inabaka shawara karka yarda kasa mai Sauki

Misali Karka yarda kasa farkon lambar wayar ka guda 4 A’matsayin pin din ka na banki , Misali Ace pin dina na banki insaka farkon lambata misali 0906 Tofa Dan Uwa indai irin Wannan pin kake sawa A’matsayin pin dinka na Bank Account din ka tofa maganar gaskiya kana ruwa, Domin ‘yan YAHOO suna hada lamba su bincika ta insun gano an bude Account da ita tofa suna irin wancan hasashen na na neman pin din ka Acikin lambar wayar ka sukan gwada hudun farko KO kuma na karshe KO kuma na tsakiya, Muddin Suka dace tofa gaskiya kafada ruwa Domin kuwa duka zai iya kwamushe ma kudin Account naka , Dan haka gara kasa password mai wahala Wanda baya daga cikin jadawalin lambar wayar ka

Haka zalika duk wani Password naka na sada zumun ta ka/ki dinga sa mai wahala ta yadda ba dama kananun Hackers su iya kutsa maka/ki Account

Abun da yake ban mamaki nasha leka password din wasu na Facebook sai inga wasu sunsa sunan mahaifiyar su, Wasu kuma sunan Budurwar su Wasu kuma sunan saurayin su Wasu kuma sunan mijin su wasu kuma Sunan matar su Wasu kuma ranar hauhuwar su Wasu kuma sunan mahaifin su Wasu kuma Sunan garin su Wasu kuma susa Nickname nasu,,, Danai binciken sai na gano duka wai sunayin hakan ne badon komai ba sai Dan karsu manta ta yadda ai baza su taba mantawa ba, Alhalin basusan hakan hatsari bane Domin su kananun Hackers ta hakan ne suke iya kutsawa Account din ka/ki , ,, Dan haka Ina mai baka/ki shawara ka/ki daina sa irin wadancanpassword din

Kudinga sa Strong Password misali irin Wannan👇

Misali inzan sa password mai wahala to sai insa kamar haka,👉

*#7+&$ To irin Wannan Password din shi yakamata ka/ki dinga sawa hakan zaifi maka/ki,,, Indai ka/ki SAKA irin Wannan zaiyi wuya Ama Hacking Account naka/ki

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url