Wanda yafi kowa kai ƙara a duniya

 

Wannan shine Mr Jonathan Lee Mutumin Da Yafi Kowa Kai Kara a Duniya


Jonathan har mahaifiyarsa ya shigar da kara a Kotu,  inda ya fada ma kotu cewa mahaifiyar ta sa bata bashi kulawa yadda ya kamata ba,  akarshe dai Mr Jonathan ya samu nasara akan mahaifiyarsa inda ta biyashi $20, 000.


Bayan wannan nasara ce Mr.Jonathan ya shigar da amininsa, da makocinsa, da wasu daga cikin yan uwansa,  da budurwarsa,  da yan sanda,  sannan ya shigar da karar wani alkali,  da wani company karshe har tsohon shugaban Amuruka George Bush ya shigar kara kuma duk ya sami nasara,  a takaice dai ya shigar da kara sau 2600.


Daga baya aka sanya sunan Mr. Jonathan Lee a matsayin wanda yafi kowa shigar da kara a littafin tarihin nan na World Guinness Book Record,  ganin sunansa acikin wannan tarihi Mr.Jonathan ya shigar da karar Guinness Book of Record gaban kotu bisa rubuta rayuwarsa acikin littafin ba tare da amincewarsa ba,  kuma ya samu nasara da kudi har $8, 000, 000


Bayan samun wannan nasara ne wani gidan tv ya nemi Mr Jonathan domin tattaunawa ta musamman,  suka tambaye shi mai yasa yake rayuwa shi kadai bashi da masoyi ko daya,  nan take Mr. Jonathan ya fara dariya ya mike tsaye ya fice, yayiwa kotu tsinke inda ya shigar da karar gidan TV bisa cin mutuncinsa akan yi masa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa domin tozartashi inda kotu ta ci tarar gidan TV $50, 000.


Masu Comment kuyi hattara kada yakaiku Kara.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url