BUDURWA A FACEBOOK


WATA BUDURWA A FACEBOOK 
ta ga  hoton wani saurayi, ya sha ado sai ta tura masa saqo.
   Kamar haka.!
   BUDURWA: “Barka da war haka Mr Abdul, wankan ka yana birge ni, ɗan wane gari ne kai ?
  SAURAYI: “Nagode ni ɗan garin kaduna ne, amma yanzu a kano nake da zama, 
ke fa ?”
  BUDURWA: “Ƴar kano ce ni, amma wace irin harka kake yi ne a kano ?”
  SAURAYI: “bana harkar komai”
  BUDURWA: “kenan dai kai student ne?”
  SAURAYI: “A'a tun ina yaro ne na gudu daga makaranta, kawai zaune nake a wani gida, Amma fa kin birge ni.”
  BUDURWA: “Nagode, ni kuma cikin satin nan aka kawo kayan aure na.
Amma fa gaskiya ina tausaya ma, rayuwa a garin da ba na ku ba, kuma gashi baka da aikin yi.”
  SAURAYI: “A'a kwanannan nake so na fara wata harka cikin $100 millions da mahaifi na ya bar min na gado”
  BUDURWA: “wow, ni kuma cikin satin nan wani abu ya hada ni da wanda ake so a mana aure, don yanzu haka ba ma tare.”
  SAURAYI: “ohh ikon Allah baya qarewa, ni kuma a cikin satin nan akayi gobara a gidan da nake, har da kudi na cikin dakin da wuta ta ci.”
  BUDURWA: “wayyo, Allah ya sauya ma da mafi alheri, na tausaya maka, ka cigaba da addu'a. 
Nima haka nayi tayi, har na samu muka dawo kamar bamu taba samun matsala ba, ni da wanda zan aura”
  SAURAYI: “to ai jakar da kudin suke ciki ba tayi komai ba, don Ko sisi bai ƙone ba, inshaAllah gobe harka kawai zan kama, so nake na zama dan chanji.”
  BUDURWA: “Da kyau Allah ya taimaka, amma kasan abun Al'ajabi ?, dazu da kaga na jima banyi ma reply ba, saƙo aka turo min wai wanda zan aura ya rasu.”
       
  Wai a cikin su wa yafi kwarewa a fagen yaudara. ?
 Just to break the silence, fatan zamu nishaɗantu! da labarin.
mu haɗu a comment▽

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url