Fake Alert

 

       Ka karanta har ƙarshe zai maka amfani

Na daɗe ina neman tayaya akeyin transfer ta ƙarya zuwa Bank Account ɗin mutum wato "fake alert" kamar yadda dai madamfara keyi ayayin da suka sayi kayan mutum suka masa transfer bayan wasu awanni da anduba account balance sai aga babu kuɗi... 


Wato transfer ta ƙarya (fake alert) ashe abune mai sauƙin gaske sai dai kawai sirrintawa da akeyi saboda kar kowa ya iya yawan ɓarayi su ƙaru, ko kuma ɓarayin basuso agano tayaya suke wannan aika aika? 


Ya zama dole ni nafada maku musamman a irin wannan lokaci da kowani cinikayya ya kusan zama harkar transfer, amma kai da zanfaɗawa na faɗa maka ne domin ka kare kanka daga faɗawa hannun waƴannan madamfara, adan haka kaji tsoron Allah kaima karda kace zaka gwada (wannan yasa ba'a faɗi saboda kar yawan azzalumai su ƙaru). 


Wato shi "fake alert" transfer ta ƙarya zuwa asusun ajjiyar kuɗin mutum ta banki ana yinsa ne akan wani Application mai suna "PRO BANK" shima kamar suffar Mobile Banking yake dashi musamman masu amfani da Mobile Bank App sunsan yadda procedure ɗin amfani da App ɗin yake. 


Shi wannan PRO BANK App ɗin akansa ake tura transfer ta kuɗi ko ince alert zuwa kowani Bank Account amma bayan anturawa mutum bayan wasu awanni kuɗin zasu ɓace, sannan alert ɗin na da wasu ɗabi'u kamar haka: 


1. Shi wannan fake alert ɗin sau ɗaya (1 time) kawai ake iyayi a rana, idan kayiwa mutum ɗaya shikinan sai kuma after 24hrs kafin ya kumayi. 


Dalili kuwa shine; dama anyi sane domin pretend/joke/ irin kayiwa mutum transfer ta ƙarya cikin wasa a tunaninsa gaskiya ne amma sai dai kawai wasa ne, kamar irin su April fool dai haka... To saboda kar amaida abin ya wuce wannan manufar shiyasa aka tsara App ɗin da sau ɗaya kawai mutum zai iya transfer ɗin a rana. 


2. Idan akai maku transfer; idan kuka duba ALERT message ɗinku na transaction ɗin to a wajan "DES" za kuga ansa "PRO" ko "PRO bank", shi wannan "Des" address ne na inda aka turo kuɗi, kamar yadda idan kaje wajan mai POS zakaga yasa sunan POS ɗin, idan ATM ne ya rubuta sunan ATM ɗin, haka idan Mobile Banking ne ya rubuta, to haka shima za kuga an rubuta "pro bank" a wajan, to da zaran kaga "PRO BANK" a wajan ka tabbata fake translation ne. 


3. Shi wannan credit translation ɗin na "fake alert" kawai ta SMS yake zuwa amma baya zuwa ta Gmail account da sauran dukkan hanyoyin da kuke receiving transaction NOTIFICATION messages na Bank naku, sannan da zaran alert ɗin ya shigo zakuga balance naku na baya da kuma kuɗin da aka turo da kuma total balance naku (to anan wajan ne za kuga kamar alert din gaske domin komai da kuke gani ayayinda aka turo maku da kuɗi bai canza ba). 


HANYOYIN KARIYA 


Duk lokacin da aka turo maku da kuɗi a banki (Credit alert transaction); 


1. Kuyi checking account balance naku direct, kusa code da ake duba balance na kuɗi zai baku normal balance na kuɗinki, karkuyi believing da SMS na wannan transaction ɗin. 


2. Kuyi ƙoƙari ku sami Mobile Banking Application na bankin da kuke amfani dashi ku ɗaura akan Smart phone naku kuɗinga amfani dashi musamman masu business, shi wannan App ɗin kai tsaye zakaje profile naka ka duba Total balance na kuɗinka, sannan ka duba transaction statement na kuɗin dukda aka turo maka ( fake alert baya zuwa kai tsaye zuwa asusun ajiyar kuɗinka na banki, sannan shi wannan App ɗin zai nuna maka ne current status naka babu ragi babu ƙari), to duk sanda wani ya turo maka da kuɗi ka duba Mobile Banking App ɗinka a take a wajan zai nuna maka gaskiyar lamari kuɗinka ya shiga ko bai shiga ba. 


3. Akwai LEO Banking system shi wannan amma na Whats'App ne sannan UBA na sani suna dashi bansan ko wani banki suma na dashi ba, shi kamar yadda kake chatting da contacts naka akan Whats'App shima haka zaku dunga chatting dashi amma computer ne, zaka duba balance, zaka tura kuɗi, sannan zaka duba statement, to shima baya ƙarya (fake alert baya hawa kansa) da zaran anturo maka da kuɗi to ka duba balance naka ta wajan zai baka real balance naka. 


Phone number ne da UBA sukayi generating wanda zakai saving akan contact naka ya fito maka ta Whats'App kamar dai sauran numbers naka to amma computer ne number din. 


4. Hanya ta ƙarshe, kafin mutum ya maka transaction idan yana kusa dakai ka tambaye sa ta ina zai turo maka da kuɗin? Ya nuna maka App ɗin da zaran kaga PRO BANK application ne to karka yarda fake alert za'a maka, sannan da zaran alert ya shiga kaga message ka duba wajan "Des" kamar yadda na faɗa a baya da kaga pro ko pro bank a wajan to fake alert ne. 


Ko wani Banki nada Mobile Banking Application nasu,  adan haka ku kula sosai... 


Allah ya daɗa karemu daga sharrin azzalumai. 


By SIR SYDDEEQ

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url