KARIN MAGANA IV
Karin Magana IV
- A cikin ido, ake tsawirya.
- A yarda ƙullon mangwaro, a huta da ƙuda.
- Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba.
- Abin da yawa, mutuwa ta je kasuwa.
- Abin kasuwa, na mai ciniki ne.
- Akuya, bata gasa da kura.
- Albarkacin kaza, ƙadangare ka sha ruwan kasko.
- Ashe ana tsoron inna? In ji 'ya'yan mayya.
- Ba a fafe gora, ranar tafiya.
- Ba a haɗa gudu, da susar ɗuwawu.
- Ba ka cin rama, sai 'yaryaɗi.
- Bakin rijiya, ba wajen wasan makaho ba ne.
- Bakina, ƙanin ƙafata.
- Bani in baka, shi ne tanka.
- Banza girman mahaukaci, ƙaramin mai wayo ya fi shi.
- Banza, ta kori wofi.
- Baya, ba zane.
- Bikin Magaji, baya hana na Magajiya.
- Biyu, tafi ɗaya ko a rabon ɗauki.
- Ci naka in ci nawa, ba rowa ba ce.
- Ciki, mai manta kyautar jiya.
- Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne.
- Da haihuwar yuyuyu, gwara/gara/ƙwara ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara.
- Da me, kurna ta fi magarya?
- Da muguwar rawa, gwanda/gwamma ƙin tashi.
- Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi.
- Duba mini hanya, makaho ya so tsegumi.
- Farar aniya, laya.
- Gajen haƙuri, shi yake kawo me aka shuka.
- Garin masoyi, ba shi da nisa.
- Ginshiƙin dutse, kowa ya yi karo da kai shi ka faɗi.
- Girma da arziƙi, ita ke sa a ja sa da abawa.
- Gobe ma, rana ce.
- Gwano, baya jin warin jikinsa.
- Hadarin ƙasa, maganin mai kabido.
- Hanci, bai san daɗin gishiri ba.
- Hangen Dala, ba shiga birni ba.
- Idan amarya bata hau doki ba, ai ko ba a ɗora mata kaya ba.
- Idan mutum ya yi nisa, baya jin kira.
- Idan ɗan kaciya bai ci kaza ba, ai ba ya yi bara ba.
- Ido ba mudu ba, ya san kima/ƙima.
- In dama ta ƙiya, sai a koma hagu.
- In ka ji ana raka ni kashi, ba zawayi/zawo ba ne.
- In ta bi daga-daga, na ƙurya ka sha kashi.
- Ina ruwan bebe da harara.
- Inda jahilci ya yi kauci, sakarci ne ya zo zai nuna ilimi.
- Jaki, yana dukan taiki.
- Jelar raƙumi, ta yi nesa da ƙasa/raɓa.
- Jiya, ta fi yau/ Da me, jiya ta fi yau?
- Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta.
- Kai mai kashe maciji, sai ka yi niyya ka ɗauki sanda.
- Kaska raɓi mai jini, ki bar shi da gashi.
- Kasuwa, a ka miki/maki dole.
- Kasuwa, akwashin Allah.
- Kaɗan, mai ban haushi.
- Kaza mai 'ya'ya, ita ke gudun shaho/shirwa.
- Kazar kwanci, ƙirjinki ya saba da danna.
- Kifin fadama, baya gasa da na kogi.
- Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.
- Kowa ya ɗora miya, sai ya nemo abun kaɗi.
- Kyawun ɗan ƙwarai, ya gaji ubansa.
- Magana, jari ce.
- Maganin kar a yi, kar a soma.
- Mai zuciya ake gayawa biki, ba mai zani ba.
- Mai zuma ya zo, mai maɗi sai ya naɗe tabarmarsa.
- Masallacin kura, ba a baiwa kare limanci.
- Masallacin kura, mai yawan ƙasusuwa.
- Maza, dangin gurjiya sai an fasa akan san bidi.
- Meye gamin kifi da kaska?
- Na Allah, baya ƙarewa.
- Na zangi, moriyarka da nisa.
- Na zaune, bai ga gari ba.
- Nan gani nan bari, farar tumfafiya.
- Ƙadangaren bakin tulu, a karka a kar tulu, a bar ka ka ɓata ruwa.
- Ƙarfe duka ƙarfe ne, amma a cikin ƙarafa akwai zinari da azurfa.
- Ƙasar kago, ta maida kago ce.
- Rigakafi, ya fi magana.
- Rumbun ƙasa, a tashi a barka.
- Sake reshe, kama ganye.
- Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya miƙa kai ya yi kallo.
- Shirim, ba inuwa.
- Sun fi kusa, Auyo da Haɗeja.
- Ta fari, ta rago.
- Ta faru ta ƙare, an yiwa mai dami ɗaya sata.
- Ta leƙo, ta koma.
- Taron na ayya, gayyar banza.
- Tashi da wuri, shi kan hana gira toho.
- Taura biyu, basa taunuwa a baki ɗaya.
- Tsiga tsiyau, kazar matsiyaci.
- Tsugunne, bata ƙare ba.
- Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farin gashinta.
- Wanda bai san Allah ba, sai wuta ta ƙona shi.
- Ɗan kuka, mai jawowa uwarsa jifa.
- Ɗinyar makaho, ta nuna a hannunsa.
- Ya ɓace ɓat, kamar ɓatan dabo.
- Yabon kai, jahilci ne.
- Yanzu-yanzu, sai Allah.
- Yautai mugun tsuntsu, masha miyarka sai ya yi dare.
- Yaɗin mage, kowa ya ci ka sai ya yi amai.
- Zaman duniya, iyawa ne'.