KARIN MAGANA III
Karin Magana III
- A rina, an saci zanen mahaukaciya.
- A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.
- Abun dariya, kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa.
- Allah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida.
- Allah, ya kawo baƙon da zai ci da ɗan gari.
- Amfanin zunubi, romo.
- An ce da ido wa ka raina? Ya ce wanda na ke gani yau da kullum.
- Ana bikin duniya, ake na kiyama.
- Ba cas, ba as.
- Babban goro, sai magogin ƙarfe.
- Bakin da Allah ya tsaga, ba zai hana shi abinci ba.
- Ban ci nanin ba, nanin ba za ta ci ni ba.
- Ban ga ta zama ba, an saci ɗan ɓarawo.
- Ban sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.
- Baya ganin zalau, sai ya leƙa.
- Cikina kwarkwaro, cikina tashiya.
- Cil-da-cil, ganin annabin tsohuwa.
- Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.
- Da mai kama, ake ƙota.
- Da sauran rina, a kaba.
- Da wuya ta kashe ka, gwara/gwanda daɗi ya kashe.
- Duk wanda ya samu rana, sai ya yi shanya.
- Duniya, rawar 'yanmata na gaba ya koma baya.
- Fankam-fankam, bata kilishi.
- Faɗan da ya fi ƙarfinka, mai da shi wasa.
- Ga bikin zuwa, babu zani.
- Ga fili, ga mai doki.
- Gaba kura, baya siyaki.
- Gaba ta kai ni, gobarar titi.
- Gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah.
- Garaje, ga dami.
- Guntun goro, ya fi babban dutse.
- Gurin da ba ƙasa, nan ake gardamar kokawa.
- Haka ma arziƙi ne, ka yi baƙo ya kashe ka.
- Idan ba a yi sharar masallaci ba, a yi ta kasuwa.
- Idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta, shafawa naka ruwa.
- Idan ka ga mutum yana shinshina/sinsina takalami, so yake ya ɗauka.
- Idan mafaɗin magana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne.
- Idan maye ya manta, uwar ɗiya bata manta.
- Idan tururuwa ta so lalacewa, sai ta fara gashi.
- Ihunka, banza.
- Ka ƙi naka dubu/duniya ta so shi.
- Kallon kitse, ake yiwa rogo.
- Karambanin baƙo, ya shiga yaƙin masu gari.
- Kare da kuɗinsa, sai ya sha lahaula.
- Karo ɗaya, ko da ƙwai da dutse a yi.
- Kasada, cinikin tsuntsu a sama.
- Kasuwar da ba a gayyace ba, daɗin ci gare ta.
- Komai aka yi da sabara, sai ta yi kere.
- Kuturu da kuɗinsa, al-kaki sai na ƙasan langa.
- Kwaɗayi, mabuɗin wahala.
- Kyautar shigo ɗaka, ka yi kuka.
- Kyawun ɗan maciji, banza.
- Magana, zarar bunu.
- Mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce kanku ake ji, ni wanka na na ke yi.
- Mai kamar zuwa, akan aika.
- Me ya fi lafiyata, cin tsiren mata.
- Mugun nufi, baya kashe ɗan barewa.
- Mutum baya ƙin ta mutane, an ce da ɓarawo ya gudu.
- Na yi maka ciki, na yi maka goyo!
- Na zo kenan, zuwa sojan badaskare.
- Ƙaramar danga, daɗin tsallaka.
- Ƙuruci, dangin hauka.
- Ragon malam, ga kyau ga araha.
- Ratsa unguwa, a haifi kamarka.
- Ruwa, ya ƙarewa ɗan kada.
- Ruwan da ya buge ka/dake ka, shi ne ruwa.
- Ruwan da ya tafasa, baya tsoron ƙuna.
- Ruwan dare, gama duniya.
- Sa'a, ta fi gata
- Sa'a, ta fi sammako.
- Sa'a, tafi manyan kaya.
- Sarki goma, zamani goma.
- Sayen biri, ba igiya.
- Shiru ka ke ji, malam ya ci shirwa.
- So, mai hana ganin laifi.
- Ta guntso, za ta fesar.
- Ta yaro, kyau take bata ƙarko.
- Tauraruwa mai wutsiya, ganinki ba alheri.
- Taɓa kiɗi, taɓa karatu.
- Tsintacciyar mage, ba ta mage.
- Tsuntsu daga sama, gasasshe.
- Tusa, ta ƙarewa bodari.
- Wanda ruwa ya ciyo shi, in aka miƙa masa takobi sai ya kama.
- Wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai yi nesa da ita.
- Wari ya ke yi, an ce da makaho ga ido.
- Wuce gona, da iri.
- Wuce makaɗi, da rawa.
- Ɗan gata, masha wuyar wata rana.
- Yaushe rabon duniya, da ayya-raye!
- Yaro, masomin babba.
- Yunwa, ba a mata lahaula.
- Zama lafiya, ya fi zama ɗan sarki.
- Zuwa da wuri, ya fi zuwa da wuri.