KARIN MAGANA II
Karin Magana II
- A tambayi kalwa zaƙin miya, a tambayi barkono a sha labari.
- Abokin damo, guza.
- Abokin ɓarawo, ɓarawo ne .
- Abun kiriki bai gaji kare ba, in ya yi ma dukansa ake yi.
- Aikin da babu lada, a bari a jingine shi.
- Allah a baki, amma a zuci sheɗan.
- Allah ɗaya, gari banban.
- Allah, ya maida ƙoƙo masaki.
- Allura, ta tono garma.
- An san da wuyan biri, ake ɗaure shi a ƙugu.
- An yi gudun gara, an faɗa gidan zago.
- An yi min sagegeduwa.
- Ba a aikin banza a Kano.
- Ba a raba harshe da haƙori.
- Ba wahalalle, sai mai kwaɗayi.
- Ba wan, ba ƙanin.
- Babu maraya, sai rago.
- Bashi ga tsuntsu, ba shi ga tarko.
- Biri, tumakan banza.
- Buƙatar maje hajji, sallah.
- Da safe, ake kama fara.
- Da zafi-zafi, akan daki ƙarfe.
- Daga ganin sarkin fawa, sai miya ta yi zaƙi.
- Dalili, mai sa a leƙa gindin surika.
- Dodo ɗaya ake yiwa tsafi.
- Dogo da hankali, da ce ne.
- Duk gautar, ja ce/Kowace gauta ja ce.
- Duk kanwar, ja ce.
- Duk wanda ya ce wutar kara ta kwana, to ya kwana bai yi barci ba.
- Duk wanda ya ce zai haɗiyi gatari, riƙe masa ƙota.
- Duk wanda ya sayi rariya, ya san za ta zubar da ruwa.
- Duk wanda ya sayi tsintsiya, yasan za ta yi shara.
- Duk wanda ya ɗebo da zafi, bakinsa.
- Duk ɗan da ya hana uwarsa barci, to shima bai runtsa ba.
- Fankan-fayau.
- Fitar barden guza.
- Ga zara ga wata.
- Garin gyaran gira, an tsole idanu.
- Goɗiyar sanƙira, a hauki a riga ki tashi.
- Haihuwar guzuma, 'ya kwance uwa kwance.
- Hali, abokin tafiya.
- Hali, zanen dutse.
- Hamburin hangun/hamburin hayam.
- Hana wani, hana kai.
- Holoƙo, hadarin kaka.
- Idan juninka sammako, to wani a tafe ya kwana.
- Idan maraya ya ji ana yiwa mai uwa faɗa, sai ya kasa kunne.
- Idan rana ta fito, tafin hannu bai iya kareta.
- Idan wani ya taka rawa aka bashi kuɗi, in wani ya taka duka zai sha.
- Ikon Allah, sai kallo.
- In da rai, da rabo.
- In ta yi ruwa, rijiya in bata yi ba masai.
- In za ka faɗi, faɗi gaskiya komai ta ja maka ka biya.
- In za ka gina ramin mugunta, gina shi gajere.
- Ina ruwan biri da gada.
- Iya ruwa, fidda kai.
- Jifan gafiyar ɓedu.
- Kafi mai kora shafawa.
- Kainuwa, dashen Allah.
- Kallo hadarin nesa, ya sa an yi wanka da kashi.
- Kallon hadarin kaji.
- Kanwa, uwar gami.
- Kere na yawo, zabo na yawo, wata rana za a haɗu.
- Kowa ya ci da mai, kuɗinsa.
- Kowa ya ci ladan kuturu, zai yi masa susa.
- Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha.
- Kowa ya ci zomo, ya ci gudu.
- Kowa ya tuna bara, bai ji daɗin bana.
- Kowace ƙwarya, da abokin burminta.
- Kulɓa na ɓarna, ana cewa jaɓa ce.
- Kura, ga kwaɗayi ga tsoro.
- Kura, ga tsoro ga ban tsoro.
- Laifin yaro ƙiwa, laifin babba rowa.
- Lauje, cikin naɗi.
- Mai rabon ganin baɗi.
- Mai tarkon tsuntsaye, baya ɗaga kara.
- Mai tsoron ta mutu, shi yake maho.
- Ƙaiƙayi, koma kan masheƙiya.
- Ƙuda, wajen kwaɓayi akan mutu.
- Ƙwarya, ta bi ƙwarya.
- Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare ya yi hankali.
- Ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba.
- Sai an gwada, akan san na ƙwarai.
- Sata gidan ɓarawo, rance.
- Shege, ka fasa.
- Ta fi nono, fari.
- Ta nan muka faro, kuturu ya ga mai ƙyasbi.
- Takunkumi, ya fi ƙarfin bakin kaza.
- Tuna baya, shi ne roƙo.
- Wake ɗaya, shi ke ɓata gari.
- Ya daɓa wuƙa a cikinsa/ya daɓawa cikinsa wuƙa.
- Ya ɗebo ruwan, dafa kansa.
- Ya yi amai, ya lashe.
- Zafin nema, baya kawo samu.
- Zakara, bada ƙwaya ka ci tsakuwa.
- Zakaranka, raƙuminka.
- Zama da maɗaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.
- Zuma, ga zaƙi ga harbi.
- Zuru, ta ishi ɗan kunya.