KARIN MAGANA V
Karin Magana V
- 'Yar bori, ba ta kallon bori.
- Abincin wani, gubar wani.
- Aikin banza, harara a duhu.
- Aikin banza, shafa lalle a ɗuwawu.
- Aikin banza, tura agwagwa cikin ruwa.
- Allah ga mu gare ka, bawan sarki ya rasa doki.
- Ba a baki na ba, an ce banten sarki ya jirge.
- Ba a hana ma bada rago, fata.
- Ba a sake wa tuwo, suna.
- Ba don mahauci ba, da mai taro bai ci naman saniya ba.
- Bakin Rijiya, ba wajen wasan yara ba ne.
- Ban ci kasuwa ba, rumfa bata faɗa min ba.
- Ban gane ba, an yi yamma da kare.
- Baƙar fura, ana gama ki mai gida na mutuwa.
- Bin umarni, waiwayen makaho.
- Biri da gatari, hasarar mai gona.
- Da alheri, uwar kishiya ta hau kura.
- Da kamar wuya, a dafa kaza a jefar.
- Da na sani, ƙeya ce.
- Da ruwan ciki, ake jan na rijiya.
- Domin kifin baɗi, ake wanke tunkunya.
- Duk wanda ya ce bai iya kuka ba, uwarsa ce bata mutu ba.
- Duk wanda ya ce garinsu da nisa, ba a kama shi ya kuɓu ce ba.
- Farilla, tusa a cikin barci.
- Farin cikin ɓarawo, ya taras da ƙofa buɗe.
- Fuska, ita ke sayar da riga.
- Gaɗar giwa, toro ke buga ganga.
- Ikon Allah, kare da tallan tsire.
- Ina sane, karuwa ta taka matar aure.
- Jiya ba yau ba, in ji tsohuwa ta ga kuɗin tsarince.
- Jure fari, na mai akuya ne.
- Kafin a yi ɗaran, aka yi kwanɗi.
- Karambanin akuya, ya saka ta leƙa ɗakin kura.
- Kayan amale, ya fi ƙarfin jaki.
- Ko biri ya karye, sai ya hau runhu.
- Komai baƙin cikin ɗan tsako, ba zai ci ɗan shirwa ba.
- Kura-ta-ci-kura.
- Kyawun saurayi, ya auri budurwa.
- Lange-lange, mai ramar ƙeta.
- Mai bunu a gindi, baya kai gudunmawar gobara.
- Mai rawar kai, baya ɗigirgire.
- Mai tsoron ta mutu, shi yake maho.
- Me na sama ya ci, balle ya baiwa na ƙasa.
- Me za a fasa? Mutuwa ko hisabi?
- Mu je zuwa, mahaukaci ya hau kura.
- Mutu ka raba, takalmin kaza.
- Naman da ya fi kusa da wuta, shi ya fi saurin gasuwa.
- Nesa-nesa, kallon kurar Jatau.
- Nono ya sake hali, mage ta sha tinya.
- Ƙawancen gaskiya, a yi shi da wando.
- Ƙazantar da ba a gani ba, sunanta tsafta.
- Ragamar damisa, a jaki da nisa.
- Randar cikin ɗaka, Allah ke ba ki ruwa.
- Raƙumi uban gararanba, kowa ya sake ka sai ya nemo ka.
- Rashin jini, rashin tsagawa.
- Rashin mutunci biki ne, kowa ya yi maka ka rama masa.
- Rikicin duniya, da mai rai ake yi.
- Ruwan kashe gobara, ba zaɓi .
- Sabon salo, gemu a kafaɗa.
- Sakarci, dukan kura da gwado.
- Sakarci, jiran jirgi a tashar mota.
- Sakarci, tura agwagwa a ruwa.
- Sandar dukan gurgu, yana kallo ake saro ta.
- Sani asali, shi saka kare cin alli.
- Saniyar da ba ta da jela, Allah ke kore mata ƙuda.
- Sara ɗaya, shi ke da bishiya.
- Shegen sama, kura tahangi biri.
- Tafiya ta tashi, ƙuad ya ga mai tallen tsire.
- Tashin hankali, ba a sa maka rana.
- Tsautsayin tauna, maye ya ci jariri.
- Tsohuwar mota, ga shan mai ga aiki.
- Tsugunne ba ta ƙare ba, an sayar da kare an sayi mage.
- Tunku, ya san jiɓar da ya ke yi wa kashi.
- Tuntuɓe, daɗin gushi.
- Turancin ungulu, sai sarkin fawa.
- Tusa, ba ta hura wuta.
- Umma, umma biyu, ta fi umma ɗaya.
- Ungulu, ba kazar kowa ba ce.
- Ungulu, ta koma gidanta na tsamiya.
- Walbisi, in ji kare da ya taka sisi.
- Wanda ba shi da doki, ba ya ƙyamar jaki.
- Wanda bai nom aba, ba ya ƙyamar awo.
- Wanda ya ci da kansa, shi ne sarkin noma.
- Wawa ana sonka, amma ba a son haihuwar ka.
- Wawa, dariyarka abin da dariya.
- Ɗan agola, mai wuyar ban nama.
- Ɗan maciji ya fi ɗan kura tsiya.
- Ɗiɗiricin balaga, kiran miji da akaifa.
- Yau da gobe karyar Allah, komai gudun mutum ta kamo shi.
- Yau da kallo, gobe da labari.
- Yawan shekaru, ba shi ne wayo ba.
- Zubar da miyau, masomin hauka.
- Zubar da yawu, masomin hauka.
- Zuma, sai da wuta.