YADDA ZAKA KARE BANKIN KA DAGA HACKERS (MADATSA)

 

Assalamu alaikum warahmatullah barkanmu da sake saduwa daku a wani sabon shirin namu wanda yake zuwa muku a wannan shafi namu mai albarka wato sirsyddeeqnews.blogspot.com, a yau muna tafe muku da yadda zaka kare asusun bankinka daga sharrin hackers wato masu kutse, Idan kabi wayannan hanyoyi insha Allah ka tsira daga sharin Hackers.

Kayi amfani da Strong Password a account naka na banki, kamar alphanumeric da kuma special characters wato ka hada Alphabet ABCD Zuwa Z, Numbers 1234 da kuma Special Characters kamar su @#$& da sauransu. Misali

MhaZ#/@90$.


Karka sa sunan ka, date of birth ko phone number naka a matsayin password naka.


Kayi amfani da Two-Factor Authentication (2FA) domin ka samu tsaro a asusun bankin ka, wanda sai an tura maka Code a phone number naka ko antura maka message a email, Wanda sai ka bayar da Code din sannan a maka kutse din


Kayi amfani da Updated antivirus software, firewalls, sannan ku saka strong password a Wi- Fi da Hosport naka


Ka kula sosai da phishing scams, wanda za'a tura maka text message a email ko phone number a bukaci bayanan ka, ko ace ka kira wannan number ko an bukata karka bayar


Ka dena shiga ko wane irin website da login details naka in har ba ka tabbatar site din mai kyau bane

Kayi amfani da official Apps na bankin ka wanda zaka yi downloading daga playstore ko app store, kar kayi downloading app daga unknown sources


Ka ringa duba bank account naka ta hanyar checking duk wani abun da kake zargi ko baka yadda dashi ba, sannan kayi reporting da wuri da zarar kaga wani abun da baka aminta dashi ba,


Ka guji sharing personal information naka ko financial information wa kowa, musamman a waya ko kuma internet.


Allah yasa a dace

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url