Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa Iran yanzu ta kai wani matsayi mai matukar hadari

 

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa Iran yanzu ta kai wani matsayi mai matukar hadari, inda ya ce kasar na da cikakken karfin kai hare-hare har zuwa cikin nahiyar Turai, lamarin da ke kara tayar da hankalin kasashen duniya baki daya.


‎Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai birnin Arad da ke kudancin Isra’ila, inda aka kai hari da makami mai linzami. A yayin ziyarar, ya yi karin haske kan yadda Iran ke kara bunkasa karfin sojinta musamman a bangaren makamai masu linzami masu nisan gaske.

‎A cewarsa, Iran ta harba wani makami mai linzami mai nisan kusan kilomita 4,000 zuwa Diego Garcia, abin da ya nuna cewa yanzu tana da ikon kai hari zuwa wurare masu nisa sosai, har ma da manyan biranen Turai.

‎Ya ce, “Na dade ina gargadi cewa Iran na kokarin samun wannan karfi, kuma yanzu sun samu damar kai hari har cikin Turai.” Ya kara da cewa har ma sun taba kai hare-hare zuwa wasu wuraren Turai kamar Cyprus, wanda ke nuna cewa barazanar ta wuce yankin Gabas ta Tsakiya.

‎Netanyahu ya kuma zargi Iran da kai hare-hare kan wuraren fararen hula da kuma wuraren ibada masu tsarki. Ya ambaci cewa an kai hari kusa da wuraren ibada na manyan addinai guda uku a Kudus — Wurin Bango na Yahudawa, Cocin Holy Sepulcher na Kiristoci, da kuma Masallacin Al-Aqsa na Musulmi.

‎Ya ce duk da wannan hari, an samu kariya ta ban mamaki inda babu wata mummunar illa da ta samu wadannan wurare, amma ya jaddada cewa manufar harin ita ce kai hari kai tsaye kan wuraren ibada, abin da ke kara nuna hadarin da ake fuskanta.

‎Bugu da kari, Netanyahu ya zargi Iran da kawo cikas ga harkokin makamashi na duniya, musamman ta hanyar tasirin da take da shi a mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur a duniya.

‎A cewarsa, abin da Iran ke yi yanzu ba kawai rikici bane na yankin Gabas ta Tsakiya, illa ya zama babban barazana ga tsaron duniya baki daya, saboda tasirin da hakan ke da shi ga tattalin arziki da zaman lafiya.

‎Saboda haka, ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su hada kai da Amurka da Isra’ila domin daukar matakan da suka dace wajen dakile wannan barazana kafin ta kara tsananta.

‎Ya jaddada cewa, “Wannan barazana ba ta tsaya ga wani yanki ba, illa tana shafar tsaron duniya gaba daya,” yana mai gargadin cewa lokaci ya yi da za a dauki mataki mai karfi.

Next Post Previous Post

⚠️

Header is warning

SisyNews 24 warning: Copying, right-clicking, or dev tools is not allowed.