Ba Zan Iya Zama da El-Rufai a Jam’iyya Ɗaya Ba — Na Shirya Ficewa Daga SDP
SANATA WADADA: Ba Zan Iya Zama da El-Rufai a Jam’iyya Ɗaya Ba — Na Shirya Ficewa Daga SDP
Sanata Ahmed Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattijai, ya bayyana niyyarsa ta barin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) tare da komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Keffi, jihar Nasarawa.
Wadada ya ce dalilin da ya fi rinjayar wannan shawara shi ne zuwan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, cikin jam’iyyar SDP.
A cewarsa, ba zai iya yin jam’iyya ɗaya da El-Rufai ba, duba da bambancin da ke tsakaninsu a fannin akidar siyasa.
"Duk da cewa Malam El-Rufai yayana ne, amma ba na jin zan iya zama da shi a jam’iyya guda saboda shi ba dan siyasa ba ne," in ji Wadada.
Sanatan ya ce yana da matukar mamaki da rashin fahimtar dalilin da ya sa El-Rufai ya bar jam’iyyar APC, wacce ta kawo shi mulki, tare da barin Shugaba Bola Tinubu wanda ya taimaka masa sosai a siyasar Najeriya.
Ya ce kasancewar El-Rufai cikin SDP babban kalubale ne ga mutanen da suka gina jam’iyyar da zuciya daya, tare da jajircewa ga manufofin da suka bambanta da na wasu 'yan siyasa da ke da niyyar amfani da jam’iyyar don son rai.