MARYAM ABACHA: Mijina Bai Yi Sata Ba

 



MARYAM ABACHA: Mijina Bai Yi Sata Ba, Duk Kudaden da Ya Tara Sun Yi Batan-Dabo

Maryam Abacha, matar tsohon shugaban soja na Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha, ta musanta zargin da ake yi wa mijinta na boye kudaden haram a kasashen waje, tana mai cewa duk abin da ya tara wa kasa ya ɓace ne bayan rasuwarsa.


A wata hira da gidan talabijin na TVC ya gudanar da ita, wacce jaridar TheCable ta ruwaito, Maryam Abacha ta ce akwai bukatar kawo tabbatacciyar shaida da ke nuna cewa mijinta ya sace kudi ya kuma boye su a waje.


"Wa ne ya gani da idonsa? A ina aka ga kudin? Ka kawo shaida ko takarda da ke nuna kudin na wajen ne," in ji Maryam.


Janar Sani Abacha ya shugabanci Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998, kafin ya rasu a ranar 8 ga watan Yuni, 1998.


Sai dai gwamnatin tarayya ta ce an kwato wasu daga cikin kudaden da ake zargin Abacha ya ajiye a bankunan waje. Rahotanni sun nuna cewa tun daga 2020 an kwato sama da dala biliyan 3.624 da ake dangantawa da tsohon shugaban.


Maryam Abacha ta yi zargin cewa ana yin shiru game da kudaden da mijinta ya bari wa Najeriya da sunan ci gaba, amma an wawashe su cikin kankanin lokaci.


"Kudin da mijina ya bari wa kasar nan, cikin 'yan watanni sun ɓace. Amma babu wanda ke magana a kai. Sai dai a ci gaba da zarginsa da sata," in ji ta.


Ta kuma bayyana cewa yadda ake ci gaba da zargin mijinta, duk bayan shekaru da rasuwarsa, alamar rashin adalci ne da ke nuna yadda matsalolin kabilanci da bambancin addini ke jefa Najeriya cikin rikice-rikice.


"Me yasa kuke dora wa wani laifi ba tare da hujja ba? Ko dai kabilanci ne ko bambancin addini ke janyo hakan? Wannan ba adalci ba ne," ta jaddada.

Next Post Previous Post

⚠️

Header is warning

SisyNews 24 warning: Copying, right-clicking, or dev tools is not allowed.