Wike Ya Sanya Sunan Tinubu a Babbar Cibiyar Taro ta Ƙasa a Abuja


 DA ƊUMI-ƊUMI: Wike Ya Sanya Sunan Tinubu a Babbar Cibiyar Taro ta Ƙasa a Abuja


Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sanar da sauya sunan babban dakin taro na cibiyar kasa da kasa da ke Abuja zuwa Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre, domin girmama shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.


Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da sabuwar cibiyar taron, inda shugaban kasa Tinubu da kansa ya jagoranci bikin bude ta a Abuja.


Ministan ya ce ginin na zamani ne wanda ke bukatar kulawa da gyara na kai tsaye, kuma hakan yana bukatar tsari da tanadi mai kyau.


A cewarsa, da yardar shugaban kasa, an yanke shawarar cewa duk wanda zai yi amfani da wannan cibiya dole ne ya biya kuɗin haya, komai matsayinsa a gwamnati ko kamfani.


“Wannan cibiyar ba za a yi amfani da ita kyauta ba. Duk wanda ke so ya yi taro a nan, sai ya biya kuɗi. Wannan ne tsarin da shugaban kasa ya amince da shi,” in ji Wike.


Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya, yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin nuna girmamawa, wasu kuma na kallon hakan a matsayin gaggawar kulla tarihi kafin lokaci.

Next Post Previous Post

⚠️

Header is warning

SisyNews 24 warning: Copying, right-clicking, or dev tools is not allowed.