YAN NAJERIYA DA KE KASASHEN WAJE ZA SU BIYA N80,000 DOMIN SAMUN BVN


Images from NIBSS

 YAN NAJERIYA DA KE KASASHEN WAJE ZA SU BIYA N80,000 DOMIN SAMUN BVN


Hukumar da ke kula da bayanan banki (NIBSS) ta sanar da cewa daga yanzu, 'yan Najeriya da ke kasashen waje za su rika biyan Naira 80,000 domin samun Bayanan Bankin Kansu (BVN).


Wannan sabon tsarin ya shafi duk wani dan Najeriya da ke zaune a ketare da ke bukatar bude asusun banki a Najeriya ko sabunta bayanansa. NIBSS ta bayyana cewa kudin ya haɗa da duk wasu ayyuka da ake buƙata domin gudanar da rajistar.


Hukumar ta ce hadin gwiwa da wasu kamfanonin da ke da wakilai a kasashen waje ne zai tabbatar da sahihancin bayanan da ake karɓa da kuma sauƙaƙa hanyar samun BVN ga 'yan Najeriya a waje.


Sai dai wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin farashin ya yi tsada fiye da kima, duba da irin matsin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.


Wasu 'yan kasa sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba lamarin, tare da rage kudin domin bai wa kowa damar yin rajistar cikin sauki ba tare da wahala ko tsadar tafiya Najeriya ba.

Next Post Previous Post

⚠️

Header is warning

SisyNews 24 warning: Copying, right-clicking, or dev tools is not allowed.