DUKIYAR ELON MUSK TA RAGU DA $39 BILIYAN

 DUKIYAR ELON MUSK TA RAGU DA $39 BILIYAN

Gistreel, Yuni 6, 2025


Rikicin Elon Musk da Donald Trump ya rikide zuwa asarar dukiya mai yawa









A wani sabon rikici da ke gudana a kafafen sada zumunta tsakanin shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, da attajirin duniya Elon Musk, rahotanni sun bayyana cewa dukiyar Elon Musk ta ragu da kusan dala biliyan 34.


Kalaman Elon Musk: “Da ni, Trump ya ci zabe”

Rikicin ya samo asali ne daga wata tuit da Elon Musk ya wallafa, inda ya ce shi ne ginshikin nasarar Trump a zaben 2024 na Amurka. Ya ce:

“Ba tare da ni ba, da Trump ya sha kaye. Democrats da yanzu ke da ikon majalisa, kuma Republicans za su kasance 51 da 49 a majalisar dattawa.”


 Martanin Trump: Barazana da hana tallafin gwamnati

Donald Trump, cikin martaninsa, ya yi barazana da cire kwangilolin gwamnati daga kamfanonin Elon Musk da kuma soke dokar tilasta sayen motocin lantarki (EV mandate) da gwamnatin Biden ta gabatar a matsayin tallafi ta hanyar rage haraji.

“Na ce masa ya bar harkar. Na kwace dokar tilasta siyan motar lantarki da babu wanda yake so,” in ji Trump.


 Ƙaramin Tarihi: Ruwan sanyi a kasafin kudin Amurka

Trump ya ƙara da cewa soke tallafin gwamnati da kwangiloli ga kamfanonin Elon Musk zai zama wata hanya ta rage kashe kuɗaɗe a kasafin kuɗin Amurka.


Asarar Dukiya Mafi Tsanani

A cewar rahoton Bloomberg, Elon Musk ya rasa dala biliyan 33.9 a rana guda, wanda hakan ya zama ɗaya daga cikin mummunan rashin arziki da aka taɓa gani a dukiyar mutum guda a rana.


 Rikicin ya nuna yadda tasirin siyasa da kafofin sada zumunta ke shafar kasuwanci da arzikin manyan mutane a duniya.

Next Post Previous Post

⚠️

Header is warning

SisyNews 24 warning: Copying, right-clicking, or dev tools is not allowed.