Natasha Akpoti-Uduaghan Ta Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Bidiyon Zuba Jari Na Karya
LABARAI | SISYNEWS 24
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi Central a majalisar dattawan Najeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna kamar tana tallata wani tsarin zuba jari ba gaskiya ba ne.
Sanatar ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi inda ta gargadi ‘yan Najeriya da kada su fada tarkon ‘yan damfara, tana mai cewa bidiyon an kirkire shi ne domin yaudarar jama’a da kwace musu kudi.
Ta ce an sarrafa bidiyon ne daga wata hira da ta taba yi da dan jarida Seun Okinbaloye, inda masu aikata damfara suka gyara shi domin tallata wani tsarin zuba jari na bogi.
A cewarta, duk da cewa bidiyon yana nuna hotonta da kuma muryarta, amma an kirkire shi ne ta hanyar amfani da dabarun fasahar zamani domin yaudarar mutane.
Sanatar ta bukaci jama’a su yi watsi da bidiyon gaba daya, tare da guje wa duk wani tsarin zuba jari da ke da alaka da wannan bidiyo.
Ta kuma roki jama’a su rika kai rahoto ga shafuka ko dandamali da ke yada bidiyon domin a cire shi daga kafafen sada zumunta kafin mutane su fada cikin matsala.
Hakazalika, ta bukaci hukumomin tsaro da kamfanonin kafafen sada zumunta su dauki matakin gaggawa kan wadanda ke da hannu wajen kirkirar wannan bidiyo na damfara.
Masana harkokin tsaro ta yanar gizo sun dade suna gargadin ‘yan Najeriya da su rika tabbatar da sahihancin duk wani tsarin zuba jari kafin su shiga, musamman wadanda ke alkawarin riba mai yawa cikin kankanin lokaci.
SISYNEWS24 – Muna bibiya domin kawo muku karin sahihan labarai daga Najeriya da sassan duniya.
