BABBAN ABINDA MASU HACKING SUKE HADAWA JAMA'A TARKO DOMIN KWACE MASU ACCOUNT SHINE PHISHING


 Assalamu alaikum warahmatullah barkanmu da sake saduwa daku a wani sabon shirin namu da yake zuwa muku a wannan shafi namu mai albarka na hasnice.hikimatv.com shin kasan menene Phishing kuwa? Kasan hatsarin da wejen PHISHING ke dashi kuwa?

Kasan kuma yadda Azzaluman Hackers suke jin dadin PHISHING kuwa?

To bari kaji shi PHISHING wata hanyace da masu yin Hacking Suke kirkira domin danawa mutum tarko ya fada cikin sauki su Sankame Account din sa, Kai zan iya cewa yanzu in kana son Sankame Account cikin Sauki ba tare da kasha wahala ba to ka kirkiri Yanar gizo ta bogi (Website din Bogi) Da zarar ka kirkira ta hakan ne cikin sauki zaka sankamewa mutane da dama Account din su ko wanna iri ne

Masu kirkirar Yanar gizo ta bogi Wacca Akewa laqabi da PHISHING, Wanda gaskiya yanzu ba kowa ne ke tsira daga tarkon su ba muddin sun dana ma, Dalilin kuwa da yasa yanzu suke mugun dana irin Wannan tarkon Wanda har yake sanadin wasu su fada Wannan tarkon shine Masu kirkirar Yanar Gizo ta bogi Sun sauya dabara kala-kala, Wanda hakan ke mugun sa jama’a su rufta tarkon su, Daga Cikin dabarun da sukeyi shine, Akwai Kwafar wani website din sak wanda zai yi wuya ka gane ba shi bane, Domin kuwa komai zaka ga na Website din iri daya ne da zarar Tsautsayi ya debeka ka shiga shi kenan har abada Wannan Account din ya fece, Sai dai in wani madatsin ne zaka saya taa dawo da shi

Sai kuma hanya ta 2 wacce gaskiya iya na Allah ne suke hayewa Domin kuwa Hackers masu kirkirar Yanar gizo ta bogi, sun bullo da wata dabara Wacce take yawan rufta mutanen mu cikin tarko, Domin yanzu tsaron Allah yayi karanci A Zukatan mu.
Mutane basa tsaron kallon Alfasha Hakan ne yasa Madatsa masu kwamushe masu kirkirar Yanar gizon bogi wato PHISHING Suke Amfanin da hakan Wajan sa Video iskanci Acikin link din ta yadda da zarar ka shiga dan kaga Alfasha Sai dai kaji garam An sankame maka Account, Kai baka videon ba kuma gashi Account din ka ya tafi To maganar gaskiya Anfi cin nasara Akan Al’ummar mu ta wajan irin Wannan sannan kuma ina son sanar da kai wani Abu ko da kaga ni A Story na wani Abokin ka Ansa video link Ance ka shiga kaga yadda Akayiwa wata wacce takai wa saurayin ta ziyara fyade To ina baka shawara Karka shiga!

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url