KARIN MAGANA I
Karin Magana I
- A juri kai ruwa rafi, wata rana gora zai fashe.
- A kai gwauro, a kai mari.
- A saka a baka, ya fi a rataya.
- A tambayi kaza hanyar rafi? A tambayi agwagwa a sha labari.
- Abokin kuka, ba a ɓoye masa mutuwa.
- Alamar ƙarfi, tana ga mai ƙiba.
- Albasa, bata yi halin ruwa ba.
- Allah ya tsari gatari, da saran shuka.
- An yi ba a yi ba, rufin ƙofa da ɓarawo.
- An yi ba a yi ba, shuka a idon makwarwa.
- Ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa.
- Ba a yi ciki dan tuwo kawai ba.
- Ba da ni ba, gaɗa a hurumi.
- Ba girin-girin ba, ta yi mai.
- Baki da gashin wance, ba kya yi kitson wance ba.
- Bakinka, ya tsuliyarka.
- Bishiyar giginya, na nesa ka sha inuwarki.
- Ciki da gaskiya, wuƙa bata huda shi.
- Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
- Da rarrafe, yaro kan tashi.
- Da rashin kira, Karen bebe ya ɓata.
- Da rashin tayi, akan bar araha.
- Da walakin, goro a miya.
- Daki-bari.
- Dare, mahutar bawa.
- Duk girman ɗantsako, ƙwai ya fi shi.
- Duk wanda ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
- Duk wanda ya ƙona rumbunsa, ya san inda toka take tsada.
- Fallasa, auren bashi.
- Faɗan gwaggo a kofa.
- Ga maciji ana bin ja.
- Gani, ya kori ji.
- Gaskiya ɗaci gareta.
- Gutun gatarinka, ya fi sari ka bani.
- Haihuwa ɗaya, horon gindi.
- Hauka da naɗe-naɗe, ɗanwake ya ga tubani.
- Idan ana ta ɓarawo, to a yi ta mabi sawu.
- Idan ka ga tsohuwa tana rawa a kasuwa, to ta daɗe tana yi.
- Idan ka je gari ka kowa da jela, kai ma nemi ka ɗaura.
- Idan kunne ya ji, jiki ya tsira.
- Idan makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka dutse.
- Ina raba ka da yin kiwo, kana kyalla ta haihu.
- Idan ɓera da sata, to daddawa ma da wari.
- Ihunka na jiyo.
- Jiki, bai fi jiki ba.
- Jiki, magayi.
- Kafin ka ga biri, biri ya ganka.
- Kai ka faɗa? Uwar sarki a kan doki.
- Kamar da gaske, karuwa ta ga noman ɗankoli.
- Kar kaza ta tono wuƙar yanka ta.
- Komai nisan dare, gari zai waye.
- Komai nisan jifa, ƙasa zai faɗo.
- Kowa ya ci zomo, ya ci gudu.
- Kowa ya ga balbela, da farinta ya ganta.
- Kowane tsuntsu, kukan gidansu yake yi.
- Kura, ta san gidan mai babban sanda.
- Lumbu-lumbu, wutar ƙaiƙayi.
- Mahaukaciyar kasuwa, sa gabanki inda ki ke so.
- Mai guri ya zo, mai tabarma ya naɗe.
- Mai haƙuri, yakan dafa dutse ya sha romonsa.
- Mai ɗaki, shi ya san inda yake yi masa yoyo.
- Marena kaɗan, zai haƙura da babu.
- Matar mutum, ƙabarinsa.
- Matar shige bata daraja.
- Mu gani a ƙasa, an ce da kare ana biki a gidan su kura.
- Murucin kan hanya/dutse, baka fito ba sai da ka shirya.
- Na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo.
- Nesa, ta zo kusa.
- Ni ya kai, kai ya ni.
- Ƙarya fure take, bata 'ya'ya.
- Ƙofar Allah, ta fi ta cali.
- Ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki.
- Ramin ƙarya, ƙurarre ne.
- Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.
- Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya.
- Ranar wanka, ba a ɓoyon cibi.
- Ruwa, ba sa'an Kwando ba ne.
- Ruwa, baya tsami banza.
- Sa toka sa katsi.
- Sabon shiga, ɓarawo da sallama.
- Sai bango ya tsage, ƙadangare yake samun wajen shiga.
- Saki reshe, kama ganye.
- Sammakon bubuƙuwa.
- Samun duniyar ɗantsako.
- Samun na sameka.
- Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.
- Sara da sassaƙa, basa hana ganji toho.
- Shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne.
- Talaka baya tashin talaka, sai tashin talaka ya zo.
- Tsautsayin takaba. auren shiɗaɗɗe.
- Tsuntsu, duka tsuntsu ne.
- Tura, ta kai bango.
- Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho.
- Wane kare ne ba bare ba?
- Wayo, ya san na ƙi.
- Wayon a ci, an kori kare daga gindin ɗinya.
- Yaro bari murna, karenka ya kama zaki.
- Yaya gara takan yi da dutse? Sai kallo.
- Zakaran da Allah ya nufa da cara, ana muzuru ana shaho sai ya yi.